Isa ga babban shafi
Afghanistan

Afghanistan zata saki Mayaƙan Taliban a gidan yari

Gwamnatin Afghanistan ta ce nan ba da jimawa ba za ta saki wasu magoya bayan ƙungiyar Taliban su 65 da ke tsare a gidajen yarin ƙasar duk da cewa Amurka ta ce yin hakan barazana ce ga ayyukan ƙungiyar tsaro ta NATO.

Shugaban ƙasar Afghanistan Hamid Ƙarzai
Shugaban ƙasar Afghanistan Hamid Ƙarzai FARS
Talla

A cikin watan Janairun da ya gabata ne gwamnatin Afghanistan ta bayyana cewa akwai ƴan Taliban aƙalla 72 da ke tsare a gidan Yarin Bagram da Amurka da kawayenta suka kafa bayan mamaye ƙasar.

Mahukuntan ƙasar Afghanistan sun ce bayan sun gudanar da bincike sun gano cewa babu wani laifi da ke kan wuyan Fursononin 72 cikin 88, amma yanzu a cewar Abdul Shukur Jami’in Gwamnatin ƙasar za su saki fursunoni 65.

Wannan matakin dai shi zai kara gurgunce danganta tsakanin Afghanistan da Amurka bayan bangarorin biyu sun ƙi amincewa da juna akan wata yarjejeniyar tsaro da ke neman Sojojin Amurka su ci gaba da zama a Afghanistan har zuwa 2014.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.