Isa ga babban shafi
Lebanon

An kafa gwamnatin hadaka tsakanin Hezbullah da ‘Yan sunni a Lebanon

Bayan kwashe watannin goma babu tsayayyar gwamnati a Lebanon, a yau Asabar, an kafa wata sabuwar gwamnatin hadaka wacce ta ba da damar hada bangarorin da ba sa ga maciji a junansu.

Shugaban Hezbullah Sayyed Hassan Nasrallah
Shugaban Hezbullah Sayyed Hassan Nasrallah REUTERS/Khalil Hassan
Talla

Gwamnatin dai ta kunshi mambobi 24 daga bangaren Kungiyar Hizbulla da ke bin akidar Shi’a da kuma bangaren mabiya akidar sunni ta tsohon Fira Minista Sa’ad Hariri, lamarin da ba a taba ganin irin shi a kasar ba, cikin shekaru uku da suka gabata.

Lebanon na daga cikin kasashen da rikicin Syria ke kokarin mamayewa ganin yadda 'yan kungiyar Hezbullah ke marawa gwamnatin kasar baya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.