Isa ga babban shafi
Lebanon

Harin bam ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 2 a Beirut

An tabbatar da mutuwar mutane akalla 2 sakamakon fashewar bam a wata unguwa da ke birnin Beirut na kasar Labanan, kuma lamarin ya faru ne a kusa da cibiyar yada al’adun kasar Iran da ke birnin.

Harin bam a Beirut
Harin bam a Beirut REUTERS/Issam Kobeisi
Talla

Harin na yau an kai shi ne a kudancin birnin inda ‘yan Shi’a ke da rinjaye. Tashoshin talabijin a kasar sun nuna yadda fashewar ta haddasa mummunar barna ga gine-ginen da ke kusa, yayin da jami’an agaji ke ci gaba da kwashe wadanda suka sami raunuka.

Wannan dai ba shi ne na farko da ake kai wa unguwar ta ‘yan Shi’a hari a birnin na Beirut ba, inda a cikin watanni uku aka kai hare-hare akalla sau biyar tare da kashe mutane kusan akalla 60.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.