Isa ga babban shafi
Syria

Amurka ta hana wani jami’in Syria ficewa daga kasarta

Hukumomin kasar Amurka, sun haramta wa jakadan kasar Syria a Majalisar Dinkin Duniya fita daga birnin New York.

REUTERS/Brendan Smialowski/Pool (GERMANY)
Talla

Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka Jen Psaki, ta ce tuni suka sanarda jakadan wannan mataki a rubuce.

A tsawon watanni 6 da suka gabata, jakadan mai suna Bashar Ja’afari, ya ziyarci birane da dama na Amurka, inda rahotanni ke cewa yana shirya tarukan farfaganda domin kare manufofin gwamnatin Damascus.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.