Pakistan
Kotu ta rage hukuncin da aka yankewa likitan da ya taimaka aka kashe Osama
Wata kotu a kasar Pakistan ta rage yawan shekarun da aka yankewa Likitan nan, Shakeel Afridi da aka kama da laifin ya ci amanar kasa wanda ya taimaka wa Jami’an leken asirin Amurka suka gano mabuyar Osama bin Laden.
Wallafawa ranar:
Talla
A watan Mayun 2012 ne aka yankewa Afridi hukuncin daurin shekaru 33, daga bisani ne kuma bayan daukaka kara, wata kotu ta rage yawan shekaru 10, da kudaden da aka ci likitan tara.
To sai dai lauyoyin likitan da danginsa sun nemi a sake masa sabuwar Shari’a domin kalubalantar sabon hukuncin da kotun ta yanke.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu