Isa ga babban shafi
Syria

Shekaru uku ana yaki a Syria

A yau Assabar ne aka cika shekaru uku da fara rikicin Syria wanda ya lakume rayukan mutane sama da dubu dari da Arba’in. Miliyoyan mutane ne suka yi hijira zuwa kasashen da ke makawabtaka da Syria saboda rikidewar rikicin kasar zuwa yakin basasa tsakanin ‘Yan tawaye da dakarun Bashar Assad.

Shugaban kasar Syria  Bashar al-Assad
Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad REUTERS/SANA/Handout via Reuters
Talla

A ranar 15 ga watan Maris ne na 2011 aka fara kaddamar da zanga-zangar kin jin gwamnatin Basharul Assad bayan irin wannan zanga-zangar ta barke a Tunisia da Masar da Libya da Yemen.

Duk da cewa an kwashe shekaru uku, yanzu ana harin shekara ta hudu amma har yanzu an kasa samo bakin zaren kawon karshen rikicin ta hanyar diflomasiya ko matakin Soji.

Yanzu haka ma rikicin Ukraine ne ya karkatar da hankulan manyan kasashen duniya akan rikicin Syria inda sama da mutane 140,000 suka mutu.

A karon farko da aka zauna teburin tattaunawa tsakanin gwamnatin Assad da ‘Yan tawaye, tare da masu shiga tsakani na Majalisar Dinkin Duniya, baran baran aka tashi a zaman tattaunawar ba tare da samun maslaha ba tsakanin bangarorin biyu.

Wani batu da ya kara zafafa rikicin Syria shi ne amfani da makamai masu guba da kuma mayakan Jihadi da suke kwarara zuwa Syria don marawa bangarorin biyu da ke rikici a kasar.

Akwai kuma sabanin ra’ayi tsakanin kasashen Duniya game da rikicin Syria, inda Saudiya da Qatar da Amurka da kasashen Yammaci ke marawa ‘Yan tawaye baya, yayin da kuma Rasha da Iran da China ke mara wa Bashaul Assad baya. Wannan ne kuma ya sa har yanzu aka kasa sasanta rikicin Syria.

Hakan masana suke fargabar ana iya kwashe shekaru 10 ba tare da magance rikicin Syria ba kamar rikicin Vietnam da Bosnia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.