Isa ga babban shafi
Syria

'Yan kasar Syria da ke gudun hijira suna fargabar Assad ya lashe zaben kasar

‘Yan gudun hijiran kasar Syria da suka sami mafaka a wani sansanin da ke Jordan, suna bayyana fargabar in shugaba Bashar al-Assad ya lashe zaben da za a yi a cikin wannan shekarar, ba za su sami halin komawa kasar tasu ba. Yayin da yakin kasar ta Syria ke shiga shekara ta 4 a wannan kaeshen makon, da dama daga cikin ‘yan gudun hijirarn kasar, su kusan dubu 100 da ke sansanin Zaatari, suna ganin ba ranar kawo karshen yakin da ya raba su da gidajensu.Har yanzu shugaba Assa bai bayyana sha’awar takarar zabe da za a yi a watan Yuli ba, sai dai mutane da dama suna gani ba makawa zai yi takara kuma ya lashe zaben. 

Wasu 'yan gudun hijirar Syria, da suka isa sansanin Zaatri a kasar Jordan
Wasu 'yan gudun hijirar Syria, da suka isa sansanin Zaatri a kasar Jordan Reuters/Majed Jaber
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.