Isa ga babban shafi
Malaysia-China

Kasashe 25 suka shiga neman Jirgin Malaysia da ya bata

Hukumomi a kasar Malaysia sun ce yanzu haka kasashe 25 suka shiga neman jirgin kasar da ya yi batan Dabo dauke da mutane 239 sama da mako Daya da ya gabata

Masu lalaben Jirgin Malaysia da ya bata
Masu lalaben Jirgin Malaysia da ya bata news.nationalgeographi...
Talla

Ministan tsaro da sufuri, Hishammuddin Hussein, ya ce sun sake samun taimakon karin kasashe da suka shiga neman jirgin, wanda yanzu kuma ake tunanin sa tsakanin Kazakstan da Tekun India.

Wannan dai na faruwa ne a dai dai lokacin da kasar China ke sukar kasar Malaysia akan fitar da bayannai masu karo da juna kan Jirgin mai Lambar MH370 da ya bata, a yayinda masu amfani da kafaifan sadarwa na Yanar Gizo ke nuna shakku akan makomar mutanen da ke ciki lura da yanda ake kokarin cika kwanaki 10 da bacewar Jirgin.

Wata Jarida kasar China mai suna China Daily ta wallafa yanda China ke kalubalantar Malaysia akan fidda bayannai masu karo da juna akan Jirgin bayan da ya kwashe fiye da Sati daya da bacewa.

Kasar China ta ce irin bayanan da basu da kima masu karo da juna da kamfanin Jirgin da Gwamnatin kasar suka rinka fitarwa na daga cikin abubuwanda suka maida aikin binciken makomar Jirgin da wuya.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.