Isa ga babban shafi
Saudiya

Saudiyya ta dakatar da bai wa Guinea da Liberia Visa saboda Ebola

Gwamnatin Saudiyya, ta dakatar da bai wa takardar Visa domin aikin hajji da Umra ga ‘yan asalin kasashen Guinea da kuma Liberia sakamakon bullar cutar ebola a wadannan kasashe.

Dakin Kaaba
Dakin Kaaba
Talla

Kamfanin dillancin labaran kasar ta Saudiyya ya jiyo ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar na cewa an dauki wannan mataki ne domin hana yaduwar cutar ta Ebola zuwa wannan kasa a daidai lokacin da aka soma shirya karbar milyoyin mutane da za su aikin haji da Umra a kasar nan gaba kadan.

Yanzu haka dai hukumomi da dama a kasashen Afirka na ci gaba da daukar matakai domin hana yaduwar wannan cuta zuwa cikin kasashensu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.