Isa ga babban shafi
Syria

Hare haren bom sun kashe mutane 59 a Syria

Akalla mutane kusan 60 suka mutu a hare haren bom da rokoki da aka kai a biranen Damascus da Homs a Syria a yau Talata, hare haren kuma sun raunata mutane da dama. Wannan al'amarin na faruwa ne a dai dai lokacin hukumar haramta yin amfani da makamai masu guba ta duniya, ta ayyana fara gudanar da bincike akan wasu sabbin hare haren makamai masu guba da aka kai a Syria.

Tashar Jirgin kasa al-Hijaz da aka kai hari a birnin Damascus  inda a kashe mutane 8
Tashar Jirgin kasa al-Hijaz da aka kai hari a birnin Damascus inda a kashe mutane 8 REUTERS/SANA/Handout via Reuters
Talla

Yanzu haka kuma, akwai 'Yan takara guda hudu da suka yanki rijistar tsayawa takarar zaben shugaban kasa da za'a gudanar a watan gobe, domin fafatawa da shugaba Basharul Assad da ke yaki da 'Yan tawaye.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.