Isa ga babban shafi
China

Mahara sun kashe Mutane 31 a yankin Xinjiang a China

Wasu ‘Yan bindiga sun kashe akalla mutane 31 a yau Alhamis bayan sun jefa bam a wata kasuwa a yankin Xinjiang da mafi yawancinsu Musulmi ne. Mahukuntan kasar sun ce mutane da dama ne suka samu rauni sakamakon harin.

Musulmin Urumqi, a yankin  Xinjiang, a kasar China.
Musulmin Urumqi, a yankin Xinjiang, a kasar China. REUTERS/Petar Kujundzic
Talla

‘Yan bindigar sun jefa bam ne a garin Urumqi, kuma sama da mutane 90 ne suka samu rauni, kamar yadda kafafen yada labaran China suka ruwaito.

Mahukuntan China sun danganta al’amarin da Ta’addanci tare da zargin ‘Yan tawayen Kabilar Uighur.

Yankin Xinjiang ya yi fama da hare hare a baya inda ko a watan jiya wasu ‘Yan bindiga sun kashe mutane uku tare da raunata mutane da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.