Isa ga babban shafi
Syria

Syria: Wasu Shugabannin ‘Yan tawaye sun yi murabus

Shugabannin ‘Yan tawayen Syria guda 9 daga bangaren masu sassaucin ra’ayi sun yi murabus a yau Assabar saboda rashin samun isasshen tallafi daga kasashen waje a yakin da suke yi da Bashar al Assad.

'Yan tawayen kasar Syria rike da muggan makamai
'Yan tawayen kasar Syria rike da muggan makamai REUTERS/Houssam Abo Dabak
Talla

A cikin wata sanarwa, Shugabannin sun nemi afuwar ‘Yan tawaye game da matakin da suka dauka na ajiye mukaminsu.

An kwashe sama da shekaru uku ‘Yan adawa a Syria suna yaki da Bashar al Assad, yayin da kuma kasashen yammaci ke jan kafa ga matakin ba ‘Yan tawayen Makamai domin kawo karshen mulkin gidansu Assad.

Wani daga cikin Shugabannin ‘Yan tawayen Kanal Mohammed Abboud ya shaidawa Kamfanin Dillacin Labaran Faransa cewa sun yi murabus ne saboda sun lura babu wata rawa da zasu iya takawa, domin akwai bangaren ‘Yan tawayen da kasashen yammaci suka fi ba fifiko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.