Isa ga babban shafi
Masar

Amurka ta nisanta kanta daga tashin hankalin da ake a Iraqi

Sakataren harakokin wajen Amurka John Kerry ya bukaci mahukuntan Masar su dauki matakan sasantawa da bangarorin siyasa domin samun dauwamammen zaman lafiya a kasar. Haka kuma Kerry ya nisanta Amurka da rikicin Iraqi

REUTERS/Brendan Smialowski/Pool
Talla

Kerry shi ne mutum na farko daga Amurka da ya gana da shugaban kasar Masar Abdel Fatah al Sisi bayan zabensa da aka yi a cikin wannan watan.

Kuma ya yi kira ga sabon Shugaban na Masar wanda ya hambarar da Muhammad Morsi ya dauki matakan sasantawa da bangarorin siyasa a kasar tare da basu ‘yancinsu na fadin albarkacin baki.

Ziyarar Kerry kuma na zuwa ne bayan kotun Masar ta yanke wa magoya bayan Morsi da dama hukuncin kisa, matakin da ya janyo matukar bore da rashin amincewa daga bangaren magoya bayan Jam’iyyar ta ‘yan Uwa musulmi a kasar Masar.

Kerry yace Amurka zata yi aiki tare da mahukunatan Masar amma yanzu kasar tana cikin wani mawuyacin hali, wanda wannan ne babban kalubale da ke gaban Al Sisi.

Haka kuma Kerry ya nisanta Amurka da rikicin Iraqi, a cewarsa rikicin na cikin gida ne da tuntuni gwamnati ya kamata ta dauki mataki.

John kerry yace rikicin Iraqi babbar barazana ce ga gabas ta tsakiya kuma ya dace mahukuntan kasar su yi wasti da banbanci akida domin shawon kan rikicin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.