Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falesdinawa

Ana ci gaba da fito na fito a Isra'ila sakamakon kashe Bafalasdine

Yayin da tashe tashen hankula ke ci gaba da yaduwa sakamakon kashe wani Bafalasdine a kasar Isra’ila, hukumomin kasar sun ce Yahudawan nan 3 da aka kama sun amsa kai wa matashin Bafalasdinen hari. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da jama’iyyar Yisrael Beitenu ta fice daga kawancen da ta shiga da jama’iyyar Likud ta Prime Minister Benjamin Netanyahu.Yau litinin ‘yan sandan Isra’ila sun ci gaba da kokarin shawo kan tashe tashen hankulan da aka shafe kwanki 5 ana yi a yankunan dake kusa da Jurasalen, da sauran garuruwan Larabawa a kasar.Hare haren da dakarun kasar ta Yahudu ke kaiwa a Gaza, da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane 8, sun sake zafafa zaman dar dar da ake yi a yankin.Waddan hare haren ne ake gani zasu iya yin sanadiyyar fito na fito tsakanin mayakan Israilan da na Falasdinu.A wani bangaren kuma Ministan harkokin wajen kasar Avigdor Lieberman ya kawo karshen kwance, da aka shafe watanni 20 ana yi, tsakanin jama’iyyar shi ta Yisrael Beitenu da Likud, mai mulkin kasar karkashin Prime Minister Benjamin Netanyahu.Lieberman ya dauki wannan matakin ne, sakamakon hare haren da Isra’ila ke kaiwa zirin Gaza. 

Ana ci gaba da tashe tashen hankula a kasar Isara'ila
Ana ci gaba da tashe tashen hankula a kasar Isara'ila REUTERS/Ammar Awad
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.