Isa ga babban shafi
Afghanistan

Abdullah ya ce shi ya yi nasara a zaben Afghanisatan

Abdullah Abdullah, daya daga cikin ‘yan takara a zaben shugabancin kasar Afghanistan, ya yi watsi da sakamakon zaben da ke bayyana abokin hamayyarsa Ashraf Ghani ya yi nasara a zaben shugabancin kasar da kashi 56.4 cikin dari.

Abdullah Abdullah, dan takarar shugabancin kasar Afghanistan.
Abdullah Abdullah, dan takarar shugabancin kasar Afghanistan. REUTERS/Mohammad Ismail
Talla

Abdullah, tsohon ministan harkokin wajen kasar wanda kuma karo na biyu kenan da yake tsayawa takarar neman wannan mukami, ya yi zargin cewa an tafka magudi a zaben, sannan ya bayyana kansa a matsayin wanda ya yi nasara.

A ranar 14 ga watan yunin da ya gabata ne aka gudanar da zagaye na biyu na wannan zabe, inda Abdullah Abdullah ya kara da Ashraf Ghani wanda tsohon jami’in bankin duniya ne.

A daidai lokacin da Ghani ya amince a sake kirga kuri’un da aka jefa a rumfunan zabe akalla dubu 7, shi kuwa Abdullah ya ce dole ne sai an kirga na rumfuna sama da dubu 11 da yake zargin cewa an tafka magudi a cikinsu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.