Guguwar Rammasun ta yi ta’adi a Philippines
Mutane 38 aka tababtar da mutuwarsu a kasar Philippines sakamakon guguwa mai tafe da iska da ruwan saman da ta mamaye kasar tare da katse wutar lantarki. Guguwar ta yi ta’adi a Manila babban birnin kasar da wasu kauyuka.
Wallafawa ranar:
Kafin isowar guguwar gwamnatin kasar ta kwashe mutane sama da 400,000 don tsirar da su.
Kungiyar agaji ta Red Cross tace guguwar ta tafi da rufin gidaje da turakan lantarki tare da lalata dukiya da dama abinda ya yi sanadiyar rasa wutar lantarki ga daukacin mutane miliyan 12 da ke Manila.
Guguwar ta sa an rufe makarantu da ofisoshin gwamnati da kuma kasuwar hada hadar hannayen jari.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu