Isa ga babban shafi
China

Girgizan kasa ta kashe mutane 589 a China

Gwamnatin Kasar china tace adadin mutanen kasar da suka mutu sakamakon girgizar kasar da aka samu a karshen mako ya tashi zuwa 589. Ma’aikatar cikin gidan kasar tace jami’anta sun tabbatar da mutuwar 589 ya zuwa yau laraba, yayin da wasu 2,401 suka samu raunuka, Kuma gidaje sama da 800,000 suka rushe ko kuma suka lalace.

Yankin Yunnan da girgizan kasa ta shafa a kasar China
Yankin Yunnan da girgizan kasa ta shafa a kasar China AFP PHOTO/Greg BAKER
Talla

Girgizan kasar ta shafi yankin Yunnan mai tsaunuka a kudu maso yammacin kasar ne. Kamfanin dillacin labaran China ya ruwaito cewa gidaje da dama ne suka rushe tare da danganta girgizan kasar a matsayin mafi muni da aka taba gani a tsawon shekaru 14 a kasar China.

Tuni Hukumomin Kasar suka aike da dimbin ma’aikatan ceto zuwa yankin da lamarin ya faru.

Kimanin shekaru 40 da suka gabata, wata girgizar kasa mai karfin maki 7.1 ta yi sanadiyar mutuwar mutune akalla 1,400 a yankin na Yunnan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.