Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falesdinu

Wani sabon Rikici ya sake Ballewa a yankin Gaza tsakanin Isra'ila da Faledinu

Yau kasar Isra’ila ta umarci sojojinta su mayar da martani, bayan da wasu makaman rokan da aka harbo daga Gaza sun sauka a kundancin kasar.Duk wannan na zuwa ne kafin wa’adin yarjejeniyar tsagaita wutan da bangarorin 2 suka amince da ita.

©REUTERS/Ahmed Zakot
Talla

Dama dai tuni aka yi hasashen cewa ba za a iya cimma wani abin kirki ba a tattaunawar da bangarorin 2 ke yi a kasar Masar, domin tsawaita yarjejeniyar tsagaita wutar da sukka cimma, bisa yadda kasar Izraela ta yi tsayin gwamin jaki, kan kin yarda ta ja baya da taki daya, daga killace palastinawan da take yi, a yankin Gaza, a yayin da kungiyar Hamas ta ce, ita kuma babu gudu babu ja da baya a kan matsayinta, har sai Izraelar ta fice kwata kwata daga yankin

Harre haren da ‘yan kungiyar Palasdinawa ta Hamas suka kai a isara’ila sun sauka ne a birnin Beersheva, da ke kudancin kasar ta Yahudu, inda ake da kimanin mutane dubu 200.
 

Sai dai sojojin isrra’ilan sun mayar da martani har sau 4, inda suka kai hare hare ta sama a yankunan arewacin Beit Lahiya, da Maghazi da kuma Khan Yunis da ke birnin Rafah a kudancin zirin Gaza.

Wani jami’ain gwamnatin kasar ta Yahudu ya shaida wa kamfanin dillacin labarun Faransa na AFP cewa, Prime Minister Benjamin Netanyahu ne ya umarci a farwa wuraren, daya kira maboyar ‘yan ta’adda, a matsayin martani.

A halin da ake ciki kuma yau Isra’ila ta umarci tawaggar ta, da ke zaman tattaunawar da ake yi da Palasdinawa a birnin Alkahiran kasar Masar, da su gaggauta kokamawa gida, bayan barkewar sabon rikicin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.