Isa ga babban shafi
Iraq-MDD

MDD ta ce za’a binciki ta’asar kungiyar ISIS a Iraqi

Hukumar kare hakkin bil’adama ta Majalisar dunkin Duniya ta amince bai daya da shirin aika Tawagar kwararru ta musamman zuwa Iraqi domin bincika ta’asar da ‘ya’yan kungiyar ‘yan tawayen ISIS suka yi a kasar

lbc.co.uk
Talla

Wannan na zuwa ne a yayin da kasar ta Iraqin ke kashedin cewar tana fuskantar babbar matsalar ‘yan ta’adda.

Majalisar mai Mambobi 47 ta amince bai daya ba tare da jefa wata kuri’a ba, akan batun tabbatar da koken da kasar Iraqi ta gabatar, matakin da fiye da kassahe 100 suka amince da shi.

Ministan kula da kare hakkin bil’adama na kasar Iraqi Mohammad Shia al-sudani ya gayawa Majalisar irin yanda kasar ke kokawa da ayyukan ‘yan ta’adda masu keta hakkin bil’adama ta hanyar kisa da dai sauransu.

Bukatar dai ta samu amincewar Mambobin Majalisar da suka hada da Burtaniya da China da Faransa da Rasha da Amurka da dai sauran manyan kasashen Duniya.

Jakadan kasar Amurka a Majalisar dunkin Duniyar ya kara nanata cewar yanayin da ake fuskanta a Iraqi ya ta’azzara, kuma yana bukatar kulawar Hukumomi.

Alkalumman Majalisar dunkin Duniya dai sun nuna cewar akalla an kashe mutane 1,420 a kasar Iraqi a Watan da ya gabata kawai, a yayin da mutane miliyan 1 da dubu 800 suka gudu.

Majalisar dunkin Duniya dai ta bayyana samun kungiyar ISIS da aikata laifukan yaki ta hanyar tada rikicin kabilanci da na Addini, kuma matsalar kunkugiyar bata tsaya kan kasar Iraqi kurum ba, harma da yankin Larabawa baki daya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.