Isa ga babban shafi
Pakistan

Hadarin kwale kwale ya yi sanadiyyar rasa ran mutane 17 a Pakistan

Akalla mutane 17 suka mutu cikin su harda wani ango da yara kanana, biyu lokacin da wani kwale kwale dake kwashe mutanen da ambaliyar ruwa ya ritsa da su, ya kife a kasar Pakistan. Hadarin ya faru ne lokacinda kwale kwalen ke kokarin tsallake wani kogin da ya kai ya kawo.Hukumomin Muzaffargarh dake Yankin Punjab sun ce kwale kwalen ya kife ne dauke da mutane 40, bayan ceto akasarin mutanen dake ciki.Wani jami’in kula da lafiya a yankin yace an sami gawar ango day a mutu mai suna Zahid Ali, da wasu yara kanana 2.Shugaban kasar Mamnoon Hussain ya bayyana kaduwar sa da hadarin. 

Shugaban kasar Pakistan, Mamnoon Hussain
Shugaban kasar Pakistan, Mamnoon Hussain REUTERS/Faisal Mahmood
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.