Isa ga babban shafi
siriya

Birnin Konane na shirin fadawa hannun mayakan ISIS na Siriya

Manzon musamman na Majalisar dunkin Duniya a kasar Siriya Staffan de Mistura, ya bukaci kasashen Duniya da su dauki dukkanin matakan da suka wajaba domin baiwa Kurdawa mazauna birnin Kobane na kasar Syriya kariya daga mayakan da ke da’awar kafa daular musulunci a Iraki da Syria

Des Kurdes fuient les gaz lacrymogènes lancés par les soldats turcs qui tentent de les chasser de la frontière turco-syrienne près de la ville de Kobane, pour les protéger des tirs de la coalition. Suruc, le 7 octobre 2014.
Des Kurdes fuient les gaz lacrymogènes lancés par les soldats turcs qui tentent de les chasser de la frontière turco-syrienne près de la ville de Kobane, pour les protéger des tirs de la coalition. Suruc, le 7 octobre 2014. AFP PHOTO / ARIS MESSINIS
Talla

Kiran na Mistura na zuwa ne yayin da rahotanni ke cewa tuni da mayakan jihadin suka kutsa a cikin birnin na Kobane wanda ke daf da kan iyakar kasar Siriya da Turkiyya.

Idan ana iya tunawa dai ya zuwa yanzu kasashe akalla 50 ne suka mika wuya ga yakin da kasar Amurka ke yi da Mayakan jihadin da suka lashi Takobin karwa duk kasar da ta taimakawa Amurka fada da su hari.

A bayan nan ma akwai wani zargi da ya fito daga kasar Amurka da ke cewar wasu kasashen Larabawa na taimakawa mayakan na ISIS da kayan fada

Amma mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden, ya nemi afuwa daga hukumomin kasar Saudiyya, bayan ya yi zargin cewa wasu daga cikin kasashen larabawa cikinsu kuwa har da Saudiyya na taimakawa mayakan jihadi da ke yankin.

Kafin nan dai mataimakin shugaban na Amurka ya nemi irin wannan afuwa daga kasashen Turkiyya da kuma Haddadiyar Daular Larabawa wadanda suka nuna bacin ransu dangane da wannan zargi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.