Dakarun Kurdawa sun isa Kobani
Rahotanni sun ce Mayakan Kurdawan Iraqi sun isa garin Kobani dauke da makamai domin taimakawa ‘Yan uwansu kurdawan Syria yaki da Mayakan IS da suka yi wa garin kawanya. Mayakan sun ratsa n ta Turkiya. Daruruwan mutane ne suka fito saman titi suna zanga-zangar lumana a Turkiya a yau Assabar domin nuna goyon baya ga kurdawan garin Kobane a kasar Syria.
Wallafawa ranar:
Wakilin Kamfanin dillacin labaran Faransa yace kimanin mutane 1,000 ne suka hada gangamin a birnin Istanbul, Amma akwai wani babban gangami da aka hada a garin Diyarbakir, yankin da kurdawa suka fi yawa a kasar Turkiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu