Isa ga babban shafi
Iraqi

Mayakan IS sun kai wa mabiya Shia hare hare

Mayakan IS da ke gwagwarmayar shinfida daular musulunci a Iraqi sun ce su suka kai wa mabiya shi’a hare hare a Badadaza a yayin da mabiyan ke shirin gudanar da bikin Ashura. Mayakan sun dauki alhakin kai wa mabiyan na Shi’a hare hare a shafinsu na Intanet.

Bikin Ashura na mabiya Shi'a suna zubar da Jini
Bikin Ashura na mabiya Shi'a suna zubar da Jini REUTERS/Omar Sobhani
Talla

Akalla mutane 18 suka mutu a wasu hare hare bama bamai guda biyu da aka kai wa mabiya Shi’a a garin Sadr a ranar Lahadi. Haka kuma an wa mabiyan hari a runfunan da suke yada zango kafin su isa birnin Karbala domin gudanar da bikin Ashura.

Gwamnatin Iraqi ta tsaurara matakan tsaro domin kare rayukan mabiya shi’a da ke yin tururuwa zuwa cikin kasar domin bikin Ashura.

Ashura rana ce ta Bakin-ciki ga Mabiya Shi’a inda suke  juyayin mutuwar Imam Hussian Jikan Manzon Tsira (SAW). Amma duk shekara ana gudanar da bukin ne cikin fargaba da tashin hankali domin sai an zubar da jini tsakanin mabiya Shi’a da Sunni da ke adawa.

‘Yan Shi’a suna tururuwa ne a garin Karbala domin karrama Kabarin Imam Hussain) cikin juyayi wanda aka kashe a zamanin Kalifa Yazid na Umayyawa a tsakanin karni na 680 Miladiya.

Akwai dai mabiya Shi’a da dama a kasashen Iraqi da Iran da Bahrain da Afghanistan da Lebanon da Pakistan da kuma Saudi Arebiya da Syria.

Sai dai kuma a irin wannan rana mabiya Sunni suna gudanar da Azumi ne a ranakun 9 da 10 na watan Muharram inda suke ganin bukin na Shi’a ya sabawa addinin Islama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.