Hamas ta ji dadin harin da aka kai wa Isra’ila
Kungiyar Hamas ta yaba da harin da wasu ‘Yan bindiga suka kai wa Isra’ila a wajen da Yahudawa ke ibada wanda ya kashe mutane hudu. Hamas tace martani ne ga kisan Bafalasdine direban mota da aka tsinci gawarsa a ranar Lahadi.
Wallafawa ranar:
A cikin wata sanarwa, Kungiyar Hamas da ke iko a Gaza tace martani ta mayarwa Isra’ila a kan kisan Yusuf Ramuni.
A ranar Lahadi ne aka tsinci gawar Ramuni a cikin mota a rataye, a cikin wani yanayi da ‘Yan sandan Isra’ila suka danganta da kisan kai.
Da safiyar yau Talata ne kuma wasu ‘Yan bindiga suka kai hari a wajen ibadar Yahudawa a birnin Kudus tare da kashe mutane hudu.
‘Yan sandan Isra’ila sun yi zargin cewa Falasdinawa ne suka kai harin dauke da bindiga da gatari.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu