Isa ga babban shafi
Jordan

Kasar Jordan ta gindaya sharudda kamin sakin Macen kungiyar ISIS

Kasar Jordan ta bukaci kungiyar ISIS ta bata tabbacin cewar matukin Jirginta da kungiyar ta kama na a raye, a kokarin da take na sakin Sojin sa Kai Mace ‘yar kungiyar ta ISIS da kasar ta kama a baya

rfi
Talla

Idan ana iya tunawa kungiyar ta ISIS ta yi barazanar kashe matukin Jirgin Maaz al-Kassasbeh, muddin ba’a sakar mata mayakiyar jihadin nan Mace ‘yar kasar Iraqi wato Sajidah al-Rishawi ba.

Kungiyar dai na bukatar a mika Sajidah ne a wani wuri na kan iyakar kasra Turkiyya kamin ta kuma saki dan Jaridar nan dan kasar Japan Kenji Goto.

A jiya dai ne kungiyar ta ISIS ta bayar a matsayin wa’adin sakar mata da wannan matar, amma har yanzu bata bada labarin komai akan wadannan mutanen da take ci gaba da rikewa ba.

Yanzu haka dai matar shi dan jaridar na kasar Japan ta kasa hakure rashin ganin mijin nata, inda take kokawa akan halin da yake ciki tana kira ga kassahen biyu na Japan da Jordan su ceto rayuwarsa.

Jordan dai ta ce abinda take baiwa fifiko a nan shi ne, ganin wadannan mutanen sun koma gida ba tare da matsala ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.