Isa ga babban shafi
Malaysia

Malaysia: Kotu ta tabbatar da hukuncin Luwadi akan Shugaban ‘Yan adawa

Kotun Kolin kasar Malaysia ta amince da hukuncin karamar kotun kasar na samun shugaban ‘yan adawar kasar Anwar Ibrahim da laifin aikata luwadi. Amma madugun adawar ya karyata zargin wanda ya danganta a matsayin yarfe domin lalata rayuwar siyasar shi.

Kotun Malaysia ta yankewa Anwar Ibrahim Madugun adawa hukuncin daurin shekaru 5 a gidan yari akan laifin Luwadi
Kotun Malaysia ta yankewa Anwar Ibrahim Madugun adawa hukuncin daurin shekaru 5 a gidan yari akan laifin Luwadi REUTERS/Samsul Said
Talla

Alkalin Kotun Mai shari’a Arifin Zakaria ya yi watsi da bukatar Anwar na sauya hukuncin daurin da aka ma sa a watan Maris na shekaru 5 a gidan yari.

Wannan hukunci yanzu zai kawo karshen rawar da shugaban ‘yan adawan zai iya takawa a siyasar kasar.

Anwar ya taba rike mukamin Mataimakin Firimiyan kasar kafin hambarar da shi a shekarar 1990.

Hukuncin yanzu ya haramtawa Anwar kujerarsa ta Majalisa tare da haramta ma sa tsayawa takara a zaben kasar na 2018.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.