Iraq
Iraqi ba ta nemi taimakon Sojin Amurka ba
Ministan Harkokin wajen kasar Iraqi Ibrahim al Jafaari ya ce kasar ba ta bukaci Amurka ta tura ma ta sojojin kasa ba don yaki da mayakan kungiyar ISIS. Al Jafaari na bayani ne bayan ganawa da takwaransa na Australia. Ya ce wannan na a matsayin martani kan bukatar da shugaba Barack Obama ya aikewa majalisar kasar don ba shi damar tura sojoji Iraqi domin kashe shugabannin kungiyar.
Wallafawa ranar:
Talla
Ministan ya ce su ba sa bukatar sojojin kasa kuma dama sun gindaya sharuddan yakin da ake yanzu haka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu