Isa ga babban shafi

Sojojin Turkiyya sun dauke kabarin Suleiman Sha daga kasar Syria

Akalla dakarun kasar Turkiya dari shida ne suka shiga kasar Syria, don gano kabarin Suleiman Sha, tare da kwashe sojojinsu dake gadin wajen, mai dinbin tarihi. Firaiyi ministan kasar Turkiya ya bayyana nasarar da dakarun kasar suka samu na dawo da kabarin a matsayin abin alfahari ga kasar ganin yadda al’amurran tsaro suka tabarbare sakamakon yakin basasa da kasar ta Syria ta fada. Kusan sojojin dari shida ne suka kutsa a cikin Syria a wani samame da suka kai na bazata a jiya Lahadi tare da kwashe sojojin kasar mãsu tsarẽ kabarin.Fraiministan kasar ta Turkiyya Ahmet Davutoglu ya ce, manufa kasar shine nasarar kwaso sojinta tare da kuma dawo da kabarin dauke da ragowar Suleyman Shah.Sai dai kuma kutse da Turkiyya tayi ya kasance irinsa na farko tun bayan da kasar ta Syria ta fada yakin basasa a shekarar 2011. Gwamnatin Turkiyya tace ta yanke shawarar fita da sojojin da kuma dawo da kabarin na Suleiman Sha ne, saboda tabarbarewa sha’anin tsaron da yankin ke ciki, yankin da yanzu haka ke karkashin ikon yan kungiyar ISIL mai da’awar kafa daular Islama a Gabas ta Tsakiya. Gwamnatin Syria ta bayyana samamen a matsayin cin zarafi ganin Turkiya bata da izinin yin hakan abinda tace ya keta kasar ta Syria. 

Kabarin Suleyman Shah, lokacin da yake arewacin kasar Syria
Kabarin Suleyman Shah, lokacin da yake arewacin kasar Syria REUTERS/Salih Boztas/Zaman Daily via Cihan News Agency
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.