Isa ga babban shafi
Saudi

Amurka ta rufe Ofishin jakadancinta na Saudiyya

Kasar Amurka ta rufe Ofishin jakadancinta da ke a Saudi Arebia har na tsawon kwanaki 2 saboda abinda ta kira fargabar matsalar tsaro, bayan wata barazana da aka ce an yiwa ma’aikatan Mai na yankin yammacin kasar

REUTERS/Evan Vucci/Pool
Talla

Sakamakon matsalar tsaro da ake kasar Amurka ke hange a kasar Saudi Arebiya, hukumomi a kasar Amurka sun sanar da janye ma’aikatansu na Ofishin jakadancinsu da ke a Saudi Arebiya, tare da rufe ofisoshin na kwanaki Biyu.

Ya zuwa yanzu dai Amurkar ta dakatar da dukkanin ayyukan jakadanci tsakaninta da Saudi Arebiya na kwanakin Lahadi da Litinin a Jeddah da Dhahran, tana kira ga jami’anta na Diplomasiyya da su kula da kansu.

Dama dai Ofishin jakadancin kasar Amurka a Saudi Arebiya ya bayyana cewar ma’aikatan Mai nakasashen yammaci na fuskanta a Saudiyya da manufar kai masu hari.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.