Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falesdinu

Netantayahu na fuskantar kalu bale a zaben kasar Isra'ila

Yau ne ake shirin gudanar da zaben kasar Israila inda Firaminsitan kasar Benjamin Netanyahu ke fuskantar babban kalubale. Sai dai a jawabin da yayi wajen neman yakin neman zaben sa jiya Netanyahu yacce muddin aka sake zaben sa bashi ba maganar kafa kasar Falasdinu.Rahotanni daga birnin Kudus na nuna cewar ga alama Firaminsitan Israila Benjamin Netanyahu ba zai samu nasarar wanan zabe ganin yadda yake ci gaba da raba kasar Israilan da kawayen ta saboda irin matakan da yake dauka.Wannan ya hada da takun sakar da yake da shuagban kasar Amurka Barack Obama da kuma adawar da yake da yunkurin kasahsen Turai na ganin an wareware rikicin nukiliyar Iran da kuma kulla yarjejeniya da Falasdinawa domin samun dawamammen zaman lafiya.Wannan y asa Netanyahu yanzu haka ya dauki aniyar samun goyan bayan Yahudawa Yan kama wuri zauna, wajen tabbatar musu da cewar zai ci gaba da watsi da kudirin majalisar dinkin duniya na hana gine gine a Yankunan Falasdinawa da kuma alkawarin watsi da kafa kasar Falasdinu.Wannan yunkuri na his dai tuni ya gamu da suka daga sassa dabam dabam na duniya, kuma ana ganin yana iya kaow karshe wa’adin mulkin san a shekaru 6. 

Fraiministan kasar Isar'ila Benjamin Netanyahu
Fraiministan kasar Isar'ila Benjamin Netanyahu REUTERS/Baz Ratner
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.