Kotu ta yankewa ‘yar Jarida daurin shekaru 7 a gidan kaso
Wata kotu a kasar China ta yanke hukuncin daurin shekaru 7 akan wata ‘yar Jarida mai shekaru 71 bayan kama ta da laifin mika bayanan sirrin kasar ga kasashen waje.kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun yi allawadai da hukuncin wanda suka danganta a matsayin yin karan tsaye ga ‘yancin fadin albarkacin baki.
Wallafawa ranar:
‘Yar Jaridar mai suna Gao Yu tana cikin jerin fitattun ‘yan jarida 50 da cibiyar binciken aikin jarida ta karrama.
Amma kotun Beijing ta yanke mata hukuncin daurin shekaru 7 a gidan yari akan lafin mika bayananin sirrin kasar China ga wata kasa, lafin da kuma ya shafi cin amanar kasa. Kotun tace yar jaridar ta mika bayanan sirrin China ne ga Hong Kong
Amma kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun yi allawadai da hukuncin wanda suka danganta a matsayin keta hakkin fadin albarkacin baki.
Rahotanni kuma sun ce ‘Yar Jaridar ta amsa laifinta bayan ‘yan sanda sun yi barazana gad anta wanda suka kame.
A kasar China dai bangaren shari’ar kasar na gudanar da ayyukansa ne da yawun gwamnati, kuma ‘yan sanda sun harmatawa ‘yan jarida kai ga kotun da aka yanke wa Gao hukunci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu