Isa ga babban shafi
Indonesia

Wani jirgin Indonesiya ya yi saukar gaggawa

An tilastawa wani jirgin saman fasinja na kasar Indonesiya, yin saukar gaggawa a yau Juma’a bayan da masu lura da zirga zargar jiragen suka sami rahoton da ke cewa an dana bom a ciki.

Jirgin Indonesia
Jirgin Indonesia Foto: Twitter
Talla

Kamfanin dillacin labaran Faransa ya ruwaito mai magana da yawun ma’aikatar sufurin kasar ta Indonesiya J.A Barata yana cewa, bayan saukar jirgin mallakin kamfanin Batik Air a kudancin Sulawesi, sai ‘yan sanda da ke binciken bom suka hau aikin.

Har yanzu ba a fidda sakamakon binciken da ‘yan sanda suka yi ba, a jirgin mai dauke da mutane 122, da suka taso daga birnin Ambon na kudancin kasar.

A cikin sanarwar da kamfanin ya fitar yace wani fasinjan jirgin ne ya samu sakon an dasa bom a cikin jirgin, akan haka ne Jami’an jirgi suka yanke shawar saukar gaggawa saboda rayuwar mutanen da ke ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.