Isa ga babban shafi
Indiya

Kotun India ta daure Salman Khan shekaru 5

Kotun India ta daure shararren mai shirin Fim na India Salman Khan hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari bayan kama shi da laifin kisan wani mutum a lokacin da ya take shi da motarsa sannan ya tsere a 2002. Salman Khan ya buge mutumin ne da motarsa kirar SUV Land Cruiser a lokacin da ya ke cikin maye a birnin Mumbai.

Salman Khan shararren mai fitowa a shirin Fim na India
Salman Khan shararren mai fitowa a shirin Fim na India bollyarena.net
Talla

Alkali mai shari’a Deshpande yace ya kama Salman Khan da laifin sanadin mutuwar mutumin.

Rahotanni sun ce Salman Khan ya tuka motarsa Land Cruiser ne kan wasu mutanen da ke kwana a titi da dare a birnin Mumbai bayan ya kwashe dogon lokaci yana dirkar barasa a gidan giya.

Mutum guda ne ya mutu daga cikin mutanen, sannan wasu da dama sun samu raunuka a hatsarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.