Isa ga babban shafi
Pakistan

Pakistan ta rufe ofishin Save The Children

Hukumomin kasar Pakistan sun bayar da umarnin rufe ofishin kungiyar tallafawa kananan yara ta Save the Children, mai shalkwata a kasar Britaniya. Ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar da ta bayar da umarnin, ba ta fadi dalilin hakan ba, sai dai tace ta dade tana sa ido kan ayyukan kungiyar, da tace suna yi wa Pakistan zagon kasa.

Firaministan Pakistan Nawaz Sharif
Firaministan Pakistan Nawaz Sharif REUTERS/Luke MacGregor
Talla

Dama hukumomin kasar sun alakanta kungiyar da wani likitan kasar mai suna Shakeel Afridi, da aka ce kungiyar leken asirin Amurka ta CIA ta yi amfani da shi cikin shekarar 2012, ta hanyar aikin riga kafin bogi, don gano inda shugaban kungiyar Al-Qaeda Osama bin Laden ke boya, lamarin da ya sa har kaka kashe shi.

Kungiyar tace an rufe ofishinta a Islamabad ba tare da wani gargadi ba daga mahukuntan kasar.

Save The Children ta dade tana musanta zargin tana da alaka da Afridi wanda ya taimaka aka kashe Osama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.