Isa ga babban shafi
SYRIA, TURKIYA

Dubban mutane na tserewa fadan Syria

Dubban ‘yan gudun hijira na cigaba da tserewa fadan da ake tabkawa tsakanin Kurdawa da Mayakan Jihadin kungiyar IS a kasar Syria, al'amarin da ya haifar da kwararar 'yan gudun hijira a kasar Turkiya bayan sake bude iyakar kasar.

'Yan gudun hijiran Syria
'Yan gudun hijiran Syria Reuters/Antonio Parrinello
Talla

A makon daya gabata kawai akalla ‘yan gudun hijira dubu 16 ne suka shiga turkiya domin samun mafaka, adaddin daya sa kasar ta rufe iyakarta, tare da bayyana cewa ‘yan gudun hijira dake cikin bukatar agajin gaggawa ne kawai za a amince su shiga cikin kasar.

Tuni dai shugaban kasar ta Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana damuwarsa dangane da kwararar ‘yan gudun hijirar sakamakon farmakin da mayakan kurdawan ke kaiwa, al’amarin da ya ce babbar barazana ce ga kasarsa, bayan dawainiyar da kasar ke yi da yan Syria kusan miliyan 2 wandanda suka tsarewa rikici tun daga shekara ta 2011.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.