Mutane 33 sun mutu a Mumbai bayan sun kwankwadi barasa mai guba
‘Yan sanda a kasar India sun tabbatar da mutuwar akalla mutane 33 a birnin Mumbai bayan sun kwankwadi barasa mai guba da ake hadawa a cikin kasar. ‘Yan sandan sun ce akwai wasu mutane 9 cikin wadanda suka kwankwadi barasar da ke cikin mawuyacin hali.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
‘Yan sandan sun ce nan take mutanen suka kamu da rashin lafiya bayan sun kwankwadi barasar, kuma adadin wadanda suka mutu na iya karuwa, domin yanzu haka mutane 9 na can mutu-kwakwai rai-kwakwai.
Rundunar ‘Yan sandan Mumbai tace ta kama mutane uku da ake zargi sun hada barasar kuma suna kan bincike.
An dade dai ana samun mutuwar mutane a India ta hanyar kwankwadar Barasa da ake sayarwa cikin karamar kwalba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu