Isa ga babban shafi
Syria

Mutane sama da Miliyan 4 sun fice Syria

Majalisar Dinkin Duniya tace adadin ‘Yan kasar Syria da rikicin kasar ya mayar ‘Yan gudun hijira sun haura miliyan hudu yanzu haka, inda a cikin watanni 10 da suka wuce mutane miliyan guda suka gudu suka bar kasar.

'Yan Gudun Hijirar Syria sun fi yawa a Turkiya
'Yan Gudun Hijirar Syria sun fi yawa a Turkiya REUTERS/Umit Bektas
Talla

Kwamishinan ‘Yan gudun hijira na Majalisar dinkin Duniya Antonio Gutheres ya bayyana yawan ‘yan gudun hijirar na Syria a matsayin irin sa mafi girma a wannan karni.

Rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce adadin mutanen Syria da ke shiga Turkiya ya sa adadinsu mutanen kasar da ke tserewa rikicin kasar ya kai kimanin Miliyan hudu da dubu goma sha uku.

Wannan kuma na zuwa ne a yayin Turkiya da ta karbi ‘Yan gudun hijira kusan Miliyan 2 ta bayyana shirin gina wani katafaren sansanin ‘Yan gudun hijira da zai dauki adadin mutane 55,000 saboda fargabar cunkosun ‘Yan gudun hijirar Syria.

A kasar Lebanon kimanin mutanen Syria miliyan 1.17 ke gudun hijira a Kasar, yayin da Jordan ta karbi mutane 629,000.

Adadin mutanen Syria 250,000 suka tsallaka zuwa Kasar Iraqi mai fama da rikici. Masar kuma ta karbi ‘Yan gudun hijira kimanin 13,500.

Rahoton kuma ya ce sauran mutanen Syria sun warwatsu ne a sassan kasashen Afrika da Turai.

Ya zuwa yanzu wadanda aka kashe a rikicin sun haura 230,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.