Isa ga babban shafi
Yemen

Bangarorin da ke rikici a Yemen sun karya Yarjejeniyar tsagaita Wuta

Bangarorin da ke rikici da juna a Yemen sun yi watsi da Yarjejeniya tsaigata wuta da Majalisar dinkin duniya ta bukata domin ba da daman shigar da kayayakin jinkai ga miliyoyin fararan hula kasar da ke cikin yunwa.

Wasu 'yan tawayen kasar Yemen
Wasu 'yan tawayen kasar Yemen REUTERS/Mohamed al-Sayaghi
Talla

Wannan kuwa ya biyo bayan ci gaba da lugude wuta da saudiya da kawayenta ke yi akan ‘yan tawayen kasar.

A yau daman ake saran fara aiki da yarjejeniyar wanda ake saran tsaiwaita shi har zuwa ranar sallar.

Sai dai an kai hare haren 2 ne a wuraren da ‘yan tawayen mabiya Shi’a suke a titunan garin Taez, inda suka gwabza rikici da dakarun da ke biyayya ga gwamnatin shugaba Abedrabbo Mansour Hadi da ke gudun hijira.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.