Isa ga babban shafi
Bangladesh

Kotun kolin Bangladesh ta yi na'am da hukuncin kisa da aka yanke wa Chowdhury

Kotun koli a kasar Bangladesh ta amince da hukuncin kisa da aka yanke wa daya daga cikin shugabannin ‘Yan adawar kasar Salahuddin Quader Chowdhury a shekaru biyu da suka gabata, bayan ta daukaka kara kan tuhumar da ake masa na aikata laifukan yaki a zamanin yakin neman ‘yancin kai a 1971.

Salauddin Quader Chowdhury
Salauddin Quader Chowdhury
Talla

Daga cikin tuhume tuhumen da ake wa Chowdhury sun hada da kashe ‘yan hindu sama da 200.

Salahuddin Quader Chowdhury yana cikin shugabannin babbar Jam’iyyar adawa ta BNP a Bangladesh kuma wannan ne karon farko da aka kama wani shugaban Jam’iyyar da hannu a rikicin Bangladesh.

Kotun ta caji Chowdhury da laifuka guda 9 da suka hada da kisa da gallazawa da kuma fyade.

Sai dai ‘Yan adawa sun soki hukuncin tare da sukar gwamnatin Firaminista Shiekh Hasina wanda suka danganta da siyasa da kuma karya 'Yan adawa.

Bangladesh dai ta fuskanci bore daga bangaren magoya bayan Jam’iyyar ‘yan uwa musulmi bayan kotu ta yankewa shugabanninsu hukuncin kisa.

A 2010 ne dai gwamnatin Bangladesh ta kafa kotu ta musamman kan yakin samun ‘Yancin kan kasar a 1971, inda aka kiyasta cewa sama da mutane miliyan uku aka kashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.