Isa ga babban shafi
Isra'ila

Wani Bayahude ya dabawa mutane 6 wuka a gangamin Aure jinsi guda

Wani Bayahude ya daba wa mutane 6 wuka a birnin Kudus a wani gangamin masu fatawar auren jinsi guda a birnin Kudus a yammacin jiya Alhamis.

Wani Bayahude ya dabawa mutane 6 wuka a gangamin Aure jinsi guda
Wani Bayahude ya dabawa mutane 6 wuka a gangamin Aure jinsi guda REUTERS/Carsten Seibold
Talla

Bayahuden mai suna Yishai Shlissel duka-duka makaonni uku ne da sako shi daga gidan yari, bayan da aka yanke masa hukuncin dauri na shekaru 10 a gidan yari sakamakon aikata irin wannan laifi a shekara ta 2005.

Nan ta ke ‘Yan sanda suka cafke Bayahuden bayan ya dabawa mutane wuka.

Jaridun Isra’ila sun ruwaito cewa kafin hakan ta faru, Bayahuden ya rubuta wasika a Intanet yana mai yin kira ga hukumomi su haramta auren jinsi guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.