Isa ga babban shafi
Pakistan-Afghanistan

Afghanistan ta caccaki Pakistan a kan harin Kabul

Shugaban kasar Afghanistan Ashraf Ghani ya caccaki Pakistan mai makwabta da kasar ta shi, kan hare-haren da aka kai birnin Kabul a ‘yan kwanakin nan da suka hallaka kusan mutane 60.

Harin birnin Kabul
Harin birnin Kabul REUTERS/Ahmad Masood
Talla

Shugaba Ghani, ya ce abubuwan da suka faru a ‘yan kwanakin nan, sun nuna cewa har yanzu akwai sansanonin ‘yan kunar bakin wake da wurare kera bama-bamai a kasar ta Pakistan.

Ya ce Afghanistan na fatan samar da zaman lafiya, amma kuma tana karbar sakonnin yaki daga pakistan.

Tun bayan fara jan ragamar mulkin kasar a shekarar da ta gabata shugaba Ghani ke yawan sokar Pakistan kan goyawa ‘yan Taliban baya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.