China
Mutane 44 sun mutu a China
Mutane akalla 44 suka mutu sannan daruruwa suka jikkata sakamakon tarwatsewar wasu abubuwa da aka adana cikin wani shago a kusa da tashar jiragen ruwa na Tianjin da ke arewacin kasar.
Wallafawa ranar:
Talla
Kafofin yada labaran China sun ce sama da mutane 500 ke kwance yanzu haka a gadon asibiti.
Bayanai daga China sun ce fashewar ta haifar da gobara da ta kone gidaje da motoci.
Mazauna yankin da al’amarin ya faru sun ce sun ji kara mai karfi, da ta lalata gine gine.
Yanzu haka ‘Yan Sandan China sun kame Shugaban Kamfanin da ya ajiye abubuwan da suka fashe.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu