Isa ga babban shafi
Indonesia

Wani jirgin Indonesia ya bata dauke da mutane 54

Mazauna kauyen Papua da ke gabashin Indonesia sun tabbatar da cewa jirgi kasar da ya bata dauke da mutane 54 ya yi hatsari kan wani tsauni dake kusa da yankinsu, sai dai har yanzu masu bincike na kan aikin tabbatar da lamarin.

Iyalan Fasinjojin wani Jirgin Indonesia
Iyalan Fasinjojin wani Jirgin Indonesia REUTERS/Supri
Talla

A safiyar yau lahadi ne Jirgin samfurin ATR-42-300 wanda ya dauko fasinjoji daga birnin Papua na Jayapura ya ba ce a haryansa na zuwa wani yankin tsauninka da ke yammacin kasar sakamakon rashin kyawun yanayi.

kuma wadanda ke cikin jirgin sun hada da fasinjoji 49 da yara 5 sai ma’aikatan jirgin 5.

Gwamnatin kasar ta ce zai zuwa gobe litinin za ta bayar da cikakken bayanai kan jirgi domin yanzu ana kan bincike.

Kasar Indonesia dai na yawan fuskantar matsalolin hatsarin jirgin sama domin ko a disamba bara akwai jirgin kasar da ya yi hatsarin dauke da fasanjoji 162 a hanyar sa na zuwa Singapor.

Hakazalika a watan yuni da ya gabata akwai wani jirgin sojin kasar da ya rikito a wata unguwa da ke birnin Medan wanda ya kashe mutane 142.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.