Isa ga babban shafi
Thailand

An kama wani da ake zargi da harin bom a kasar Thailand

Rundunar sojan kasar Thailand tace mutumin nan da aka kama, ana zargi da hannu a harin bom da aka kai birnin Bangkok cikin makon daya gabata, baya bayar da hadin kai a binciken da ake yi.

Wani mutum da ake zargi da hannu a harin birnin Bangkok na kasar Thailand
Wani mutum da ake zargi da hannu a harin birnin Bangkok na kasar Thailand Reuters/路透社
Talla

Lokacin da yake jawabi yau Lahadi, Kwamandan sojan kasar, janar Udomdej Sitabutr, yace mutumin, dan kasar waje da ba a bayyana sunansa ba, yaki amsa tambayoyin da ake masa kan harin, da yayi sanadiyyar sara san muuatane da dama.
Masu bincike sun ce sun kama mutumin ne, yayin wani samamen da aka kai a wajen birnin na Bangkok, dauke da kayan hada bama bamai.
Sai dai kuma mahukuntan kasar ta Thailand na ci gaba da shan suka, bayan da suka muna wata rigar dake dauke da bama bamai a talibijin din kasar, wadda kuma bata da alaka da wancan harin, a lokacin da ake bayani kan kama mutumin.
Sai dai jami’an gwamnati sun ce rigar bata cikin kayayyakin da aka samu a wajen mutumin, inda suka ce kuskure gidan talibijin din yayi waje dauko hoton rigar, da bata da alaka da kamun, inda aka nemi jama’a su guji yada hoton a shafukan Internet.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.