Al-sisi ya amince da murabus din Majalisar Ministocin Masar
Shugaban Kasar Masar Abdel Fatah Al-Sisi ya amince da murabus din Majalisar Ministocin gwamantin Kasar karkashin Firai Minista Ibrahim Mehleb.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
To sai dai Shugaba Al-Sisi ya umarci Ministocin da su ci gaba da rike mukamansu kafin a a kafa sabuwar Majalisar Ministocin Kasar.
Wata sanarwa data fito daga fadar shugaban Kasar bata yi karin bayani ba kan dalilin yin murabus din,amma dai hakan na zuwa ne bayan an kama Minsitan albarkatun gona bisa zargin sa da aikata laifin cin hanci da rashawa.
Tuni dai Al-Sisi ya buakci tsohon Minstan albarkatun mai, Sherif Isma’il da ya kafa sabuwar Majalisar Ministoci nanda mako guda.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu