Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falasdinu

Rikici a Masallacin al-Aqsa ya shiga ranar ta biyu

Wani sabon rikici ya sake barkewa a yau litanin kwana na 2 a jere, tsakanin Falasdinawa da ‘yan sandan Isra’ila, a harabar babban masallacin al’Aqsa, a dai-dai wani lokaci da aka shiga sabuwar shekarar Yahudawa.

REUTERS/Ammar Awad
Talla

Majiyar ‘yan sandan isra’ila ta ce, rikicin ya balle ne a cikin harabar Masalacin na Al’aqsa sakamakon yadda wasu matasan musulmi Falasdinawa da suka rufe fuskokinsu suka shiga jifar ‘yan sandan da duwatsu

A cewar shaidun ganin da ido, wasu falasdinawa sama da 20 sun kwashe daren jiya lahadi a cikin masalacin na al-Aqsa, domin gujewa hanasu shiga masalacin a yau litanin sakamakon ziyarar da yahudawan ke yi a yau litanin

Rahotannin sun bayyana cewa daga harabar masalacin rikicin ya ba zu a wasu sassan birnin na kudus mai dadaden tarihi ga manyan addinan duniya guda uku, da suka hada da Musulunci Cristanci da kuma Yahudanci

Wakilin kamfanin dillancin labaran AFP ya ce ‘Yan sanda sun yi amfani da kulake da kuma barkonon tsohuwa, wajen tarwatsa gungun masu zanga zangar, da suka hada da tsofaffin mata da dama da ake kira "mourabitate" ‘yan asalin yankin da suka ki yarda a rabasu da kusa ga masallacin na Kudus.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.