Isa ga babban shafi
Yemen

Harin roka ya kashe angwaye a Yemen

Wasu angwaye uku na daga cikin mutane goma sha uku da su ka rasa rayukansu a harin roka da aka kai a wani kauye dake kudu maso yammancin kasar Yemen.

Saudiya da kawayenta na kaddamar na yaki da mayakan Houthi a Yemen.
Saudiya da kawayenta na kaddamar na yaki da mayakan Houthi a Yemen. AFP PHOTO / MOHAMMED HUWAIS
Talla

Wannan dai shi ne hari na uku a cikin makwanni biyu da ake kai wa akan taron jama’a da ke bukukuwa da ya kuma yi sanadiyar mutuwar farraren hula sama da dari 130.

Hakazalika wani alkalin kotu da babban hafsan soji sun rasa rayukansu bayan wasu yan bindiga akan babur sun bude musu wuta

Mutane sama da dubu daya ne suka rasa rayukansu tun bayan da Kasar Saudiya da kawayenta su ka kaddamar da yaki akan mayakan Houthi.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.