Isa ga babban shafi
Bangladesh

Mutanen Banladesh na siyar da Kodarsu saboda talauci

Taluci da rashin ayyukan yi da kuma matsalolin rayuwa sun jefa al’ummar kasar Bangladesh cikin mawuyacin hali abinda ya sa wasu ke sayar da kodar jikinsu domin samun abinda zasu ci.

Cutar koda na barazana a wasu jihohin Najeriya.
Cutar koda na barazana a wasu jihohin Najeriya. Centers for Disease Control and Prevention
Talla

Wani bincike da kamfanin dillancin labaran Faransa ya gudanar a yankin Kalai, ya nuna cewar akalla mutane 40 suka sayar da kodarsu a cikin wannan shekara don samun kudaden da zasu biya bukatunsu, kamar yadda jami’in ‘Yan Sandan yankin Sirajul Islam ya tabbatar.

Jami’in ya ce mutane 200 yanzu haka suka sayar da kodarsu tun daga shekarar 2005 a yankin, kuma da dama daga cikin su sun mutu saboda matsalar da ta biyo baya.

Wata mata mai suna Rawshan Ara mai shekaru 28 ta ce, ‘yan uwanta biyu sun gargade ta kan sayar da kodarta bayan matsalar da suka samu lokacin cire tasu, amma talauci ya sa ta tayi kunnen uwar shegu, kuma yanzu haka ta shiga cikin mawuyacin hali.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.