Isa ga babban shafi
Philippines

Guguwar Koppu ta yi barna a Philippines

Daruruwan mutane ne suka makale a gidajensu a kasar Philippines sakamakon ruwan sama da ya haifar da ambaliya da ta mamaye gidaje da gonaki tare da tafiya da dabbobi.

Guguwar Koppu ta yi barna a Philippines
Guguwar Koppu ta yi barna a Philippines AFP PHOTO
Talla

Mummunar Guguwar Koppu mai tafe da iska ce ta haifar da ambaliyar ruwan.

Ya zuwa yanzu hukumomin kasar sun ce akalla mutane 60,000 suka tserewa gidajensu, don kaucewa bala’in da aka dade ba a ga irinsa ba.

Rahotanni sun ce tuni gwamnatin kasar ta tura sojoji da jami’an kananan hukumomi da kuma masu aikin agaji kauyuka 70 da bala’in ya shafa don gudanar da aikin agaji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.