Isa ga babban shafi
Afghanistan

Girgizan kasa ta kashe mutane da dama a Afghanistan da Pakistan

Mutane kusan 300 aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon girgizar kasar da aka samu a kudancin Asia da ta ratsa kasashen Pakistan da Afghanistan zuwa India, inda ta girgiza gidaje da rusa makarantu.

Yankin Peshawar a Pakistan da girgizan kasa ta shafa
Yankin Peshawar a Pakistan da girgizan kasa ta shafa REUTERS/Khuram Parvez
Talla

Rahotanni sun ce mutane sama da 1000 suka samu raunuka yayin da daruruwan gidaje suka rushe a girgizan kasar da aka samu a ranar Litinin.

Yanzu haka masu aikin agaji na ci gaba da neman wadanda suka tsira daga bala’in girgizan kasar

Rahotanni sun ce ganin karfin girgizar kasar da kuma irin ta’adin da ta yi na rusa daruruwan gidaje da kuma girgiza garuruwa da dama adadin wadanda suka mutu na iya karuwa.

Pakistan ta tura jami’an sojinta domin gudanar da ayyukan agaji bayan mutuwar mutane 214 da kuma raunana 1,800 yayin da India da suke samun sabani tace a shirye take ta taimakawa kasar.

Rahotanni a Afghanistan sun ce yara dalibai mata 12 suka mutu daga cikin adadin 63 da suka mutu a kasar, lokacin da suke kokarin tserewa daga ginin makarantarsu da girgizar kasar ta rusa.

Masu aikin agaji sun ce ana sa ran samun wasu mutane da rai daga cikin gidajen da suka fadi.

Kungiyar Taliban ta bukaci kungiyoyin agaji su ci gaba da aikin ceto ga mutanen Afghanistan da bala’in girgizan kasa ta shafa, sannan kungiyar ta bukaci mayakanta su taimaka a wuraren da mutane ke bukatar agaji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.